SiyasaAsiya
Jakandan Amurka ya ziyarci wajen rabon abinci a Gaza
August 1, 2025Talla
Manzon Amurka Mr. Witkoff ya isa Isra'ila a wani sabon yunkurin Washington na bukatar tsagaita bude wuta a yankin Zirin Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas, kamar yadda wani jami'in gwamnatin Amurkan ya sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Karin bayani:Ministan harkokin wajen Jamus ya fara ziyarar aiki a Isra'ila
Tun da fari dai jakadan Amurka a Isra'ila Mike Huckabee ya wallafa hotunan Mr. Witkoff a shafinsa na X, a yayin da yake rangadi a sansanin rabon kayan abinci a Gaza.