Khamenei ya fito bainar jama'a bayan rikici da Isra'ila
July 6, 2025Wannan bayyanar ta faru ne a wani taron jimami da aka gudanar a masallacin Imam Khomeini da ke tsakiyar birnin Tehran, a ranar Asabar, a daidai lokacin da ake tunawa da ranar Ashura, mafi tsarki a kalandar Musulunci ta mabiya mazhabar Shia.
Khamenei, wanda ke da shekaru 86, bai yi jawabi ba a wurin taron, amma an nuna shi yana gaishe-gaishe da magoya baya da suka tashi tsaye suna rera wakoki da taken kasar Iran.
Wannan shi ne karo na farko da aka ga Khamenei a fili tun bayan barkewar rikicin da ya fara a ranar 13 ga Yuni, lokacin da Isra'ila ta kai hari kan manyan wuraren makaman nukiliya da sojojin Iran.
Khamenei dai na da kololuwar iko a dukkan harkokin gwamnati a Iran, kuma ya yi amfani da sakonnin bidiyo da aka riga aka dauka don isar da sakonni ga jama'a a lokacin rikicin.