Tanzaniya: Lissu ya zargi gwamnati da jinkirta shari'arsa
July 30, 2025Talla
Tun a watan Afrilu ne aka tsare Mr. Lissu, matakin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya da manazarta suka yi Allah wadai da shi. Hakan na zuwa ne a yayin da hukumomi ke kara matsin lamba a kan jam'iyyarsa ta CHADEMA mai adawa, gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a watan Oktoba.
Har yanzu dai karamar kotun da ke gudanar da shari'ar na zaman jiran izinin babbar kotu kafin ta ci gaba da shari'ar, saboda karfin tuhumar da Lissu ke fuskanta.
A wannan Larabar (30.07.2025) masu gabatar da kara sun bukaci kotun da ta sake dage karar, yayin da suke jiran bukatar da suka shigar gaban babbar kotun kasa, na ba su izinin bai wa shaidu kariya lokacin zaman shari'ar.