Italiya za ta taimaka wa 'yan kasuwarta
April 6, 2025Talla
Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta yi alkawarin kare harkokin kasuwancin da ke iya tabuwa a kasar saboda harajin da Amurka ta kakaba a kan kayayyakin da za su shiga cikinta.
Ita dai Firamista Meloni na da aiki a gabanta na iya daidaita gardamar diflomasiyya tsakanin kasarta da Amurka, ganin tana dasawa da Shugaba Donald Trump.
A hannun guda kuwa dai dole ne ta dauki matakan kare darajar kayayyakin Italiya da za su shiga Amurka, saboda tsarin kaso 20% kan kayayyakin kasashen Tarayyar Turai da Amurka ta tsara.
Kafofin watsa labarai a Italiyar a wannan Lahadi, sun ruwaito cewa Firaminista Meloni na iya zuwa Amurka kafin ranar 14 ga wannan wata domin tattaunawa da Shugaba Trump kan batun na haraji da ya shafi kasashe.