Italiya da Aljeriya za su aiki tare kan bakin haure
July 23, 2025A yayin taron kamfanoni sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin da suka hada da makamashi da bangaren sadarwa.
Firaministan Italiya Giorgia Meloni ta gana da shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune a fadar gwamnati ta Doria Pamphili na karni na 17, biyo bayan wata ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Antonio Tajani ya kai birnin Algiers a watan Maris.
Aljeriya ita ce babbar abokiyar kasuwancin Rome a Afirka, tare da cinikin kusan Euro biliyan 14 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 16.4, yayin da jarin Rome a kasar ya kai biliyan 8.5, a cewar Italiya.
Kazalika kasashen biyu sun amince da wani shiri na daidaita ayyukan bincike da ceton bakin haure da ke yunkurin tsallakawa teku mai hadari daga arewacin Afirka zuwa Turai. A shekarar 2022 ne aka zabi gwamnatin Meloni da nufin kawo karshen kwararar bakin haure.