Isra'ila za ta fadada matsugunan Yahudawa
May 29, 2025Isra'ila ta kwace yankin gabar yamma tare da Gaza da gabashin birnin Kudus a yakin Gabas ta Tsakiya a 1967, abin da Falasdinawan ke nema a dawo musu da yankunan uku domin kafa kasarsu.
Yawancin kasashen duniya na kallon yankunan da Isra'ila ta mamaye a matsayin haramtattu kuma cikas ga kokarin da aka shafe gomman shekaru ana yi na kawo karshen rikicin.
A shekarar 2005 Israila ta janye daga zirin Gaza amma wasu jagorori a gwamnatin yanzu suna kira a sake karbewa da ma yankin Falasdinawa baki daya a tsugunar da su a wani wuri na daban, abin da suka kira kaura na radin kai.
A waje guda kuma wani hari da Isra'ila ta kai a zirin Gaza inda Falasdinawa suke cikin mawuyacin halin bukatar abinci bayan watanni uku da ta rufe dukkan iyakoki a yankin ya hallaka a kalla mutane 13 a cewar Jami'an lafiya.