SiyasaGabas ta Tsakiya
Isra'ila ta yi luguden bama-bamai a asibitin Al Ahli na Gaza
April 13, 2025Talla
Isra'ila ta kaddamar da mummunar farmaki a guda daga cikin asibitin da ke tsaye a birnin Gaza, inda ta yi zargin cewa mayakan Hamas na boye asibitin na Baptist wanda aka fi sani da Ahli Arab.
Karin bayani:WHO na neman a kwashe mutane daga asibitin al-Shifa na Gaza
Harin na zuwa ne kwana guda da sanarwar da MDD ta yi na cewa kayan kula da marasa lafiya da magunguna sun yanke a Zirin Gaza. Wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP ya wallafa hotuna da bidiyon buraguzan asibitin na Al-Ahli da Isra'ila da lalata.