Isra'ila ta yi ikrarin kashe kwamandar Hezbollah
May 17, 2025Jami'ai a Lebanon sun ruwaito cewa, mutum daya ya mutu a hare-hare guda hudu da Isra'ila ta kai cikin 'yan kwanaki duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma. Sai dai kuma Isra'ila ta yi ikrarin cewa ta kawar da kwamanda daya na kungiyar, da ke da hannu wajen sake farfado ababen more rayuwa da kungiyar a kudancin Lebanon.
Karin bayani: Hezbollah da Isra'ila sun cimma yarjejeniya
Rundunar sojin Isra'ila ta ce, sake gina ababen more rayuwa na 'yan ta'adda da ayyukan da ke da alaka da su kamar rashin mutunta fahimtar da ke tsakanin Isra'ila da Lebanon ne. Tun dama dai a yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Nuwambar shekarar 2024, an bukaci kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran ta janye mayakanta daga arewacin kogin Litani, da kuma lalata dukannin wasu ababen more rayuwa da mayakan a kudancin kasar. A gefe guda, Firanministan Lebanon, Nawaf Salam ya bukaci a matsa lamba ga Isra'ila kan ta janye dakarunta daga dukannin yankunan Lebanon tare da dakatar da kai hare-hare.