Isra'ila ta lashi takobin ci gaba da mamaye Gaza
March 21, 2025Ministan Tsaron Isra'ila ya ce ya bayar da umarni ga sojin kasan kasarsa na nausawa can cikin zirin Gaza tare da shan alwashin kwace iko da wasu yankunan zirin idan Hamas bata saki Isra'ilawa da ke hannunta ba.
Acikin wata sanarwa Minista Israel Katz ya ce tsawon lokacin da Hamas za ta ci gaba da dauka ta na rike mutanen, shi ne tsawon lokaci da Isra'ila za ta ci gaba da mamaye zirin tare da kwace kasa.
Isra'ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a zirin Gaza
Bayan sake karbe iko da mashigar Netzarim mai matukar muhimmanci da ta raba tsakanin arewaci da kudancin Gaza, sojojin na Isra'ila sun kutsa zuwa garin Beit Lahiya da kuma birnin Rafah.
Har ila yau, sojojin suka ce daga yanzu sun koma toshe arewacin Gaza kenan ciki har ma da birnin Gazan kansa.
Harin Isra'ila ya halaka daruruwan mutane a Gaza
Tuni dai wannan yunkurin na Isra'ila ya fara shan suka a duniya inda ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya shaida wa manema labarai cewa Faransa ta na adawa da duk wani yunkuri na kwace zirin Gaza.