Isra'ila ta kutsa cikin Deir al-Balah na Gaza ta kasa
July 21, 2025A karon farko tun bayan fara yakin Gaza sojojin Isra'ila sun fara shiga cikin garin Deir al-Balah ta kasa, kamar yadda shaidu suka bayyana a ranar Litinin.
Mazauna yankin sun ce sojojin Isra'ila sun kwace gine-gine a kudu maso yammacin birnin da ke tsakiyar Gaza kuma sun saka masu harbi daga nesa a kan rufin gine-gine.
Gomman Falasdinawa sun mutu wajen jiran kayan agaji
Dakarun Isra'ila ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da wannan kutsen.
A ranar Lahadi, sojojin sun umarci mutane su fice daga wasu unguwanni a kudu maso yammacin birnin kuma mazauna sun ce sun bar gidajensu da sassafe ranar Litinin.
Merz na Jamus ya caccaki Isra'ila bisa rikicin Gaza
‘Yan jaridar da ke aiki a Falasdinu sun shaida wa BBC cewa, tankokin Isra'ila sun kutsa yankin, tare da kaddamar da hare-haren sama da na artilari.