SiyasaGabas ta Tsakiya
Isra'ila ta kashe mai magana da yawun mayakan Hamas
September 1, 2025Talla
Wani hari da sojojin Isra'ila suka kai a yankin Zirin Gaza ya halaka kakakin kungiyar Hamas Abu Obeida wanda Isra'ilan ke nema ruwa a jallo.
Karin bayani:Isra'ila ta kashe shugaban Hamas, Yahya Sinwar
Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz shi ne ya tabbatar da mutuwar Obeida a shafinsa na X, bayan Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce dakarun sojin kasar sun yi nasarar kawar da mai magana da yawun Hamas wanda kuma shi ne Isra'ilan ta kai wa farmaki.
Karin bayani:Jagoran addinin Iran ya ce mutuwar shugaban Hamas ba ta sanyaya gwiwar gwgwarmayarsu ba a Gabas ta Tsakiya
Isra'ila ta halaka jagororin kungiyar Hamas da dama a yakin da ta shafe watanni 23 tana gwabzawa da mayakan Hamas a Gaza ciki har da Yahya Sinwar da Isma'il Haniyeh.