Isra'ila ta kashe akalla mutum 25 a Gaza
May 26, 2025Likitoci a zirin Gaza ta Falasdinawa sun sanar da mutuwar akalla mutum 25 a wani harin asuba da Isra'ila ta kaddamar kan wata makaranta da aka mayar sansanin 'yan gudun hijira.
Isra'ila dai ta ce ta kaddamar da hari kan sansanin ne don kakkabe wasu "manyan 'yan ta'adda" da suka buya a sansanin da ke Gaza mai dankare da al'umma sama da miliyan biyu.
Harbin da sojojin Isra'ila suka yi, ya ja mata suka
Luguden wutan da Tel Aviv ke yi a baya-bayan nan dai ya gamu da suka daga kasashen duniya bayan toshe shigar da kayan agaji a Gaza na kusan watanni uku.
Shugabannin kasashen duniya da suka hallara a birnin Madrid na Sfaniya a karshen mako sun yi kira da a kawo karshen abinda suka kira "kashe-kashe marasa amfani."
A karshen makon nan likitoci da sauran ma'aikatan agaji sun rika zakulo gawarwakin mutane da aka kashe musamman a Jabalia da ke arewacin Gaza wurin da ya kasance fagen luguden wutan kasar ta Isra'ila.