Isra'ila ta kai hari a asibitin Naseer dake Khan Younis
March 24, 2025Harin wanda ya tada gobara a sashin gudanar da tiyata ga marasa lafiya, na zuwa ne kwanaki bayan da ya cika makil da mutane dake neman kulawar likitoci biyo bayan yakin da Isra'ila ta koma da kai farmaki ta sama da ta kasa a Gaza.
Isra'ila wace ta tabbatar da harin ta ce ta kai shi ne a kan maboyar mayakan Hamas, ta kuma dora alhakin mutuwar faraen hula a kan Hamas dake boyewa a cikin al'umma.
A sanarwar da ma'aikatar lafiya ta fitar, tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023, adadin wadanda suka rasa rayukansu a Gaza ya zuwa yanzu sun haura mutane dubu 50 baya ga darurun wadanda suka jikkata.
Sojojin Isra'ila tun bayan da suka koma yaki a Gaza sun bayyana kashe manyan kwamandojin Hamas, kazalika al'ummar Isra'ila na ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin amincewa da komawa yaki da sojoin kasar suka yi a Gaza.
Karin BayaniEU za ta je Isra'ila kan sabbin hare-hare a Gaza: