Israila ta kai hari Beirut karon farko bayan tsagaita wuta
March 28, 2025Harin wanda aka kai a wannan Juma'ar ya lalata gine-gine a wajen kudancin Beirut. A cewar ma'aikatar tsaron Israila, harin martani ne ga rokoki da aka harba a arewacin iyakokinta. Rundunar sojin ta ce ta dauki matakin ne domin lalata wani jirgi mara matuki na kungiyar Hizbullah wadda ke samun goyon baya daga Iran.
Kamfanin dillancin labaran Lebanon ya tabbatar da cewa jiragen yakin Israila sun yi barin wuta a yankin Hadath a kudancin Lebanon.Sojojin Israilar sun kuma ce sun lalata wasu cibiyoyi na Hizbullah da ke kudancin Lebanon.
Shugaban kasar Lebanon Joseph Aoun da ke ziyara a Faransa inda ya gana da shugaba Emmanuel Macron ya ce ba za lamunci hari kan birnin na Beirut ba, yana mai cewa hakan zai bayar da dama ne ga Hizbullah.
Sai dai ministan tsaron Israila Israel Katz ya ce gwamnatin Lebanon ita ce ke da alhakin duk abin da ya faru na harin, yana kashedin cewa idan ba a daina kai hari kan jama'a a yankunan Kiryat Shmona da Galilee ba su ma ba za su fasa kai hari Beirut ba.
Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon Jeanine Hennis-Plasschaert ta baiyana aukuwar musayar wuta a iyakar kudancin Lebanon da cewa abin damuwa ne kwarai.