Isra'ila ta harba makaman roka a Lebanon
March 22, 2025Hakan na zuwa ne bayan da Isra'ila ta ce ta kama wasu makaman roka da aka cillo mata ta kan iyaka, abin da ya jefa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mayakan Hezbollah da Isra'ilan cikin barazana.
Rikici tsakanin Hezbollah da Isra'ila na zama wani babban burbushin yakin da Isra'ilan ke gwabzawa da Hamas a Zirin Gaza, inda shekara guda da ta wuce aka kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra'ilan da kungiyar Hezbollah ta Lebanonmai rike da muggan makamai.
Hezbollah dai ta musanta harba wa Isra'ila makaman roka a wannan Asabar, tana mai cewa ba ta da hannu a harin domin ta dukufa wajen tabbatar da dorewar yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tsakaninta da Isra'ila.
Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wa Isra'ila harin da ka iya zama na tsokanar fada, amma wani jami'in Isra'ila ya ce makaman roka shida aka harba musu, yayin da suka yi nasarar dakile uku daga cikinsu.