SiyasaIsra'ila
Spain da wasu kasashen Turai sun gargadi Isra'ila
August 10, 2025Talla
Kasahen sun yi gargadin cewar hakan zai kara tsananta matsalar jin kai, da kuma kara jefa rayuwar mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su cikin hadari.
Baya ga Spain,ministocin harkokin wajen Iceland,da Ireland, da Luxemburg, da Malta, da Norwai, da Portugal da Slovenia suma, sun rattaba hannu kan wannan sanarwa.
Wannan sanarwa na zuwa ne, a daidai lokacin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke kare shirinsa a gaban manema labarai,
lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida, da suka hada da kawayensa masu ra'ayin rikau, da kuma kasashen duniya.
Yanzu haka dai kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa a kan shirin na Isra'ila na mamaye Gaza.