Isra'ila ta dakatar da shigar da kayan agaji Gaza
March 2, 2025Matakin Isra'ilan na zuwa ne kwana guda da cikar wa'adin farko na yarjejeniyar da Masar da Qatar da sauran masu ruwa da tsaki suka jagoranta.
karin bayani:Isra'ila ta bukaci tsawaita yarjejeniya har bayan Ramadan
Awanni kafin daukar wannan mataki, ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya amince da bukatar Amurka na tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma musayar fursunoni da kuma gawarwaki tsakanin Isra'ila da Hamas har zuwa bayan azumin Ramadan.
Karin bayani:Yarjejeniyar tsagaita buda wuta tsakanin Hamas da Isra'ila ta shiga mataki na gaba
Gwamnatin Isra'ila ta sanar da cewa ta dauki wannan mataki ne domin bai wa jakadan da shugaba Donald Trump na Amurka ya nada kan al'amuran da suka shafi Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff, damar gabatar da sabbin matakai da shawarwari kan sulhu da kuma bai wa al'ummar musulmi a Gaza damar gudanar da ibada da kuma Yahudawa da zasu gudanar da bikin Passover a watan Afrilu.
Mai magana da yawun Hamas Hazem Qassem ya fitar da sanarwar cewa kungiyar ba ta amince da bukatar tsawaita wa'adin farko na yarjejeniyar ba, abin da Hamas ta ke bukata shi ne aiwatar da daftarin farko kamar yadda dukkanin bangarorin biyu suka amince da hakan.