Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza
March 18, 2025Isra'ila ta yi alkawarin ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza har sai an dawo da dukkan 'yan kasarta da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su. Wannan barazanar na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan da cikin dare gwamnatin Benjamin Netanyahu ta kai hare-hare mafi muni tun bayan fara aiwatar da yarjejeniar tsagaita bude wuta, inda aka kashe akalla mutane 413 a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.
Karin bayani: Martani kan barazanar Trump na kwace iko da Gaza
Wannan farmakin Isra'ila na haifar da illa ga yunkurin samar da zaman lafiya mai yankin Gabas ta tsakiya, a daidai lokacin da tattaunawa kai tsaye tsakanin bangarorin da ke fada da juna ta tsaya. Sai dai wani shugaban Hamas ya tabbatar da cewa kungiyarsu na aiki da masu shiga tsakani don ja wa Isra'ila birki, lamarin da a cewarsa ya sa Hamas ba ta mayar da martani ba.
Karin bayani: Taron Larabawa kan makomar Gaza a Masar
Kasashe da dama sun yi Allah-wadai da hare-haren da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza ciki har da Masar da Turkiyya da Iran da Saudiyya. Yayin da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna kaduwa tare da yin kira da a mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da sako sauran wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da gindaya sharadi ba.