Isra'ila ta bukaci Falasdinawa su kaura zuwa wasu yankuna
September 6, 2025Talla
Yayin da Isra'ila ta ke zafafa kai hare-hare a zirin Gaza, rundunar sojin Isra'ila ta shawarci yankin na Falasdinu da su kaura domin tsiratar da rayuwarsu zuwa yankin da ake bayar da agaji a Khan Younis. A gargadin na gaggawa ga mazauna Zirin a tantunan da ke kusa da yankin da yaki da daidaita, rundunar ta ce za ta kai farmaki kan wasu gine-gine sakamkon kasancewar mayakan Hamas a gine-ginen da ke yankin ko kuma a kewaye.
Karin bayani: Falasdinawa na tsere wa yankuna Khan Younis saboda harin Isra'ila
Kakakin rundunar sojin ta Isra'ila, Avichay Adraee, ya bukaci jama'ar Zirin da su kaura zuwa Al-Mawasi, inda akwai asbibitoci da butun ruwa da ma abinci da magunguna.