SiyasaGabas ta Tsakiya
Isra'ila ta amince da tabka kuskuren halaka 'yan agaji 15
April 20, 2025Talla
Isra'ila ta amince da cewa dakarun sojinta sun tabka kuskuren halaka jami'an agaji 15 a Gaza, a cikin watan Maris na 2025.
Karin bayani:Jamus ta kwashe 'yan kasarta 24 da iyalansu daga Gaza
Haka zalika rundunar sojin ta kori kwamandan sojojin da ya jagoranci aikata kisan, sakamakon samunsa da nuna rashin kwarewa a aiki wajen gaza bayar da gamsassun bayanai na gaskiyar lamari.
Karin bayani:Isra'ila ta yi luguden bama-bamai a asibitin Al Ahli na Gaza
Jami'an kungiyar agaji ta Red Crescent 8 aka kashe a harin, sai jami'an tsaro 6 na Majalisar Dinkin Duniya da ma'aikacinta daya, a harin da dakarun sojin Isra'ila suka kai wa jerin gwanon motocinsu a yankin Tel al-Sultan na kudancin Rafah a Gaza, ranar 23 ga watan na Maris.