Isra'ila na shirin zafafa kai hare-hare a Gaza
May 17, 2025Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta fara kai sabbin hare-hare a Zirin Gaza, kana tana tattara dakarunta da nufin cimma nasarar kwace wasu yankunan Zirin. Rundunar ta kuma ce za ta cimma burinta na yaki, ciki kuwa har da kwato sauran Isra'ilawa da kungiyar Hamas ke ci gaba da tsare su a Gaza.
Karin bayani:Isra'ila za ta fadada hare-haren da take kai wa Gaza
A farkon wannan makon ne Firanministan Isra'ilar, Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kai hare-hare da karfin gaske. Kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da yin Alllah wadai da ayyukan Isra'ilar da ma matsayarta na hana shigar da agaji zuwa Zirin. Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk ya soki matakin Isra'ila ya na mai cewa hakan wani yunkuri na shafe mutane da daga doron kasa.