Isra'ila ta fadada hare-hare a kan Iran
June 13, 2025Karin wasu hare-hare da Isra'ila ke ci gaba kai wa Iran a wannan Juma'a sun yi ajalin akalla mutane takwas tare da jikkatar da wadansu mutanen 12 a yankin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar.
A cikin wata sanarwa rundunar sojojin Isra'ila ta ce tana ci gaba da kakabo jiragen marasa matuka da Teheran ta harba wa kasar a matsayin martani.
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta sa Isra'ila ta yi nadamar wadannan hare-haren da ta yi kuskuren kai wa a wannan Juma'a dalibi a cibiyoyin nukiliya. A cikin wani jawabi da ya yi wa 'yan kasar ta faifan bidiyo wanda aka watsa a kafar talabijin, Shugaba Pezeshkhian ya ce al'ummar Iran da shugabannita ba za su yi shuru su kyale wannan aika-aika ba sannan za a mayar wa Isra'ila martani mai zafi da zai sa ta yi da na sani.
Karin bayani: Harin ramuwar gayya ne mafita ga Iran?
Iran din ta kuma kira wadannan hare-hare da Isra'ila ta kai mata a matsayin ayyana mata yaki, yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya gargadin cewa da akwai karin hare-hare mafi muni da Isra'ilar ke shirin kai wa nan gaba matukar fadar mulki ta Teheran ba ta gaggauta cimma yarjejeniya kan shirinta na nukiliya ba.
A gefe guda shugabannin kasashe ko gwamnatocin Jamus da Faransa da Burtaniya sun yin wata tattaunawa ta wayar tarho a tsakiyar wannan rana ta Juma'a, biyo bayan kazaman hare-hare na Isra'ila da ka iya birkita yankin Gabas ta Tsakiya. Jim kadan bayan hare-haren shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Isra'ila na da 'yancin kare kasarta, sai dai ya yi kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.
Daga nasa bangare shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadin cewa Isra'ila na neman jefa duniya cikin gagarumin bala'i tare da kiran kasashe masu karfin fada a ji da su gagguta taka mata birki.