Iran za ta tattauna yarjejeniyar kera nukiliyarta da Amurka
April 8, 2025Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai gana da wakilin Amurka na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff a kasar Oman ranar Asabar, domin fara tattaunawar farko kan yarjejeniyar makamashin nukiliya da shugaba Donald Trump ke kara matsa mata lamba a kai.
Karin bayani:Iran ta ce Amurka za ta dandana kudarta idan ta kai mata hari
Mr Araghchi wanda ya ba da wannan tabbaci a Talatar nan yayin jawabi daga kasar Algeria ta gidan talabijin din Iran, ya ce masu shiga tsakani na Oman za su yi dawainiyar bibiyar ra'ayoyin kasashen biyu, ma'ana ba lallai tattauna wa ta kai tsaye ba, sabanin sanarwar Mr Trump ta ranar Litinin da ke cewa ta kai tsaye ce.
Karin bayani:Iran ba za ta tattauna da Amurka kan mamakin nukuliya ba
A shekarun da suka gabata an gudanar da tattaunawa makamanciyarta karkashin gwamnatin Joe Biden, to sai dai ba ta haifar da wani abin a zo a gani ba, wanda a yanzu haka Iran ta yi nisa kan kudurinta na kera makamashin nukiliya da ya kai mataki na kashi 60 cikin 100 na aiki da uranium, wanda bai yi wa Amurka da Isra'ila dadi ba, har su ke barazanar daukar matakin soji a kai.