Iran za ta gana da Turai kan shirin nukiliya
July 20, 2025Kamfanin dillancin labaran Tasnim da ke Tehran ya ruwaito cewa, an cimma yarjejeniyar kan samar da matsayar yarjejeniyoyi tsakanin Iran da kasashen Turai kan shirin nukiliyar Iran, sai da kuma ana ci gaba da tuntubar juna kan tsayar da lokaci da kuma wuri. Wasu rahotannin sun kuma yi nuni da cewa, an tsara yin wasu zaman tattaunawar a matakin ministan harkokin wajen kasar a makon gobe.
Karin bayani: Ko Iran da Amurka za su tattauna kan nukiliya?
Wannan dai zai kasance ganawa ta farko tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Iran da Isra'ila. Ko da yake kafin nan, gwamnatin Tehran ta gana da Washinghton kan shirin nukiliyar na tsawon watanni biyu. Tehran dai na fatan a soke takunkuman da aka kakaba mata, yayin da Amurka da kasashen Turai ke zargin Iran da habaka sinadarin uranium dinta zuwa makamin nukiliya. Duk da cewa Tehran ta dade tana hakikancewa shirin nukiliyarta na lumana ne.