Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan Isra'ila
June 16, 2025An wayi garin Litinin ana barin wuta tsakanin Isra'ila da Iran a yakin da ya barke tsakanin kasashen biyu a ranar Juma'a bayan Tel Aviv ta kaddamar da hari kan Tehran.
Iran ta rika ruwan makamai masu linzami kan biranen Isra'ila ciki har da cibiyar makamashi ta birnin Haifa. Ita kuwa Isra'ila ta rika luguden wuta da jiragen yaki a kan kasar Iran inda jiragen yakinta suka zazzaga bama-bamai kan ma'aikatar harkokin wajen Iran.
Masu aikin ceto a Isra'ila sun ruwaito cewa mutum hudu sun mutu sannan an lalata wasu gine-ginen da mutane ke ciki a biranen daban-daban na kasar.
Shugaba Trump na Amurka ya gargadi Iran kan yaki da Isra'ila
Iran ta ce dakarun rundunarta na juyin juya hali ne suka yi luguden wuta a Isra'ilar kuma wurare na musamman suka hara a farmakin na safiyar Litinin.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ba ta da niyyar samar da makaman nukiliya sannan tana da 'yancin fadada ayyukan nukiliyarta don makamashi tare da cewa jagoran addinin kasar ta Iran Ayatollah Ali Khamenei ba ya bukatar sarrafa makaman kare dangi.
Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a Iran
Ya zuwa yanzu dai alkaluma da suka bayyana wa manema labarai sun nuna cewa an kashe wa Iran mutum 224 a yayin da ita kuwa Isra'ila ta rasa mutum 18.